in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mayakan Al-Shabaab 11 a kudancin Somaliya
2016-11-24 10:06:08 cri

Rundunar sojin kasar Somali (SNA), ta sanar da cewa, a ranar Larabar da ta gabata ta kashe mayakan Al-Shabaab 11 a lokacin da suka yi mummunar arangama a kauyen Gof-Gadud kusa da garin Baidoa dake kudancin Somaliya.

Kwamishina na musamman a yankin kudu maso yammacin Somaliya Mohamed Isak Hassan, ya shedawa 'yan jaridu cewa, sojojin hadin gwiwa sun yi nasarar hallaka mayakan ne a lokacin da suka yi arangama tsakaninsu da 'yan tawayen.

Hassan ya kara da cewa, a lokacin da mayakan Al-Shabaab suke mafarkin sun kwace iko a yankin, sai ga shi sun yi hasarar mayakansu 11, sannan an raunata wasu da dama. Sai dai a cewarsa SNA ta yi hasarar sojojinta 3 a lokacin gumurzun.

Kwamishinan ya ce, SNA da dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika, za su cigaba da kaddamar da hare hare kan mayakan 'yan tawayen har sai ta kakkabe su daga shiyyar gabashin Afrika baki daya.

To sai dai a nata bangaren, kungiyar Al-Shabaab ta yi ikirarin cewa ita ce ta yi galaba a fafatawar da suka yi ta baya bayan nan da dakarun gwamnatain Somaliya a shiyyar arewa maso yammacin kasar, inda ta yi nasarar hallaka sojojin gwamnati 3.

Wata majiya mai zaman kanta ta ambato cewa, an samu hasarar sojojin gwamnatin da dama a lokacin artabun, da kuma wadanda suka jikkata, inda tuni aka garzaya da su zuwa asibitin garin Baidoa.

Hare haren na baya bayan nan sun zo ne a dai dai lokacin da aka tsaurara matakan tsaro a kasar Somaliya sakamakon zagayen kasar na zaben kasar da za'a gudanar a makon gobe.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China