in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi kiran da a girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Somaliya
2016-11-14 13:44:56 cri
Manzon musamman na MDD dake kasar Somaliya, Michael Keating yayi kira ga jihohin Somaliya biyu dake yaki da juna dasu amince da wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin kawo karshen tashe tashen hankali wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 54 a tsawon makwannin baya bayan nan.

Michael Keating, manzon musammun na sakatare janar na MDD a kasar Somaliya, ya bayyana cewa,aniyyar shugaba Abdiweli Mohamed Ali "Gaas" na Punland da Abdikarim Hussein Guled na Galmudug za ta bada kwarin gwiwa, amma sai an yi aiki da yarjejeniyoyin yadda ya kamata.

Ya ce, ba za a amince da take yarjejeniyar ba, kana dukkan shugabannin zasu amsa alhakin abin da ya faru, mista Keating ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Mogadishu a jiya Lahadi.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan gudanar da shawarwari a ranar Asabar, inda a yayin zaman aka samu halartar shugabannin Somaliya a karkashin jagorancin faraminista Sharmarke da abokan hulda na kasa da kasa, inda aka cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Galkayo, ta yadda za a sami wata hanyar warware rikicin.

A yayin wannan taro, shugabannin jihohin biyu dake yaki da juna, a karkashin jagorancin mista Sharmarke, sun kuduri niyyar aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin birnin da suke takadama kansa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China