Tawagar AU ta bayyana cewa wani ayarinta dake kan hanyar zuwa Ceel Buur ya murkushe wani kwanton bauna da mayakan Al-Shabaab suka shirya da kuma janyo babbar asara ga mayakan 'yan ta'adda.
AMISOM nada labarin wadannan zarge zarge na kafofin yada labarai kan mutuwar fararen hulan din a cikin dukkan ayyukansu, inda ta kara da cewa dukkan wadannan zarge zarge an yi bincike kansu tare da hukumomin Somaliya.
A cewar kafofin yada labarai, fararen hula 7 ne sojojin Habasha suka harbe a lokacin da suke aiki a cikin tawagar AMISOM. Wadannan labarai sun tabbatar da cewa dakarun AU sun yi barin wuta a yankin Dac, bayan da mayakan kungiyar Al-Shabaab suka yi musu kwanton bauna a birnin dake tsakiyar Somaliya.
Mayakan Al-Shabaab sun kara zafafa hare harensu a 'yan watannin baya bayan domin kifar da gwamnatin Somaliya da kafa wata kasar dake aiki da dokokin musulunci. (Maman Ada)