in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da farmakin da aka kai wa wani bikin jana'iza a Yemen
2016-10-10 11:02:49 cri

Babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa a shekaran jiya Asabar, inda ya yi Allah wadai da farmakin da aka kai wa wani bikin jana'iza a wannan rana a birnin Sanaa, babban birnin kasar Yemen, ya kuma yi kira da a gaggauta yin bincike kan wannan batu.

Sanarwar ta ce, bincike na matakin farko da aka gudanar ya nuna cewa, akwai yiyuwar sojojin kawance dake karkashin jagorancin kasar Saudiyya suka kai wannan farmakin ta sama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 140, a yayin da mutane da dama suka jikkata.

Ban Ki-Moon ya nuna jajantawa ga iyalan mutanen da suka mutu, da kuma fatan samun sauki ga mutanen da suka jikkata.

Ban da haka kuma, sanarwar ta ce, Ban Ki-Moon ya kalubalanci bangarori daban daban da su bi dokar jin kai ta duniya, domin kare rayukan fararen hula da kuma kare manyan ayyukan more rayuwa.

Saidai hadaddiyar rundunar sojojin dake karkashin jagorancin kasar Saudiyya ta musunta wannan zargi. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China