Bisa labaran da aka samu, an ce, shugaba Hady ya bayyana kiyayyarsa kan wannan shiri bisa dukkan fannoni a yayin wata ganawa tare da Mr. Ahmed a birnin Riyadh na kasar Saudiya a ranar Asabar.
Haka kuma, wani shafin intanet na kasar Yemen ya ruwaito maganar shugaba Hady cewa, shirin zaman lafiya da MDD ta gabatar ba zai samar wa kasar Yemen zaman lafiya ba, illa kawai zai bude wata kofa ta daban ga al'ummomin kasar shiga cikin karin barazana da rikice-rikice.
A halin yanzu, ba a yi bayani kan shirin zaman lafiya da Mr. Ahmed ya gabatar ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun bayyana cewa, ana fatan kafa wata gwamnatin hadin gwiwa a tsakanin gwamnatin kasar da jam'iyyar adawa cikin wannan shiri. (Maryam)