in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da ke kamuwa da cutar Kanjamau da masu dauke da kwayoyin cutar ya kai dubu 654 a kasar Sin
2016-12-01 11:41:45 cri

Yau ranar 1 ga watan Disamba rana ce ta yaki da cutar kanjamau ta duniya, kuma babban take na ranar ta bana shi ne "hadin gwiwa don yaki da cutar kanjamau, kuma a mai da hankali kan rigakafi". Bisa kididdigar da aka samu daga cibiyar shawo kan cututtuka ta kasar Sin, an ce, ya zuwa watan Satumba na shekarar 2016, yawan mutanen da ke kamuwa da cutar kanjamau da masu dauke da kwayoyin cutar ya kai dubu 654 a kasar Sin, kuma yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai dubu 201. Yin jima'i wata muhimmiyar hanya ce ta yada cutar, kuma yawan matasa da tsoffi da ke kamuwa da cutar yana ta karuwa cikin sauri.

Haka kuma kididdigar ta nuna cewa, a watanni tara na farkon shekarar bana, an yi bincike ga mutane miliyan 120 kan cutar kanjamau a duk fadin kasar Sin, inda aka gano cewa, sabbin mutanen da ke kamuwa da cutar ya kai dubu 96, kashi 94.2 cikin dari daga cikinsu kuwa yawanci kamu da cutar ta hanyar yin jima'i.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China