in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane dubu 497 ke rayuwa da ciwon Sida a Sin
2014-12-01 12:23:50 cri

Mukaddashin darektan hukumar lafiya da tsarin iyali ta kasar Sin, Wang Guoqiang ya ce, a karshen watan Oktoba, adadin wadanda ke dauke da kwayar AIDS mai karya garkuwar jikin bil'adama a kasar Sin ya kai dubu 497, kuma kamar yadda ya ce, daga ciki an samu wadanda suka rasa rayukansu, a sakamakon cutar wadanda adadin su ya kai dubu 154.

Wang ya bayyana hakan ne a wajen wani kamfe na wayar da kan jama'a, jawabin nasa ya nuna an samu karin adadin yawan masu dauke da cutar a kasar ta Sin. Wang ya kara da cewar, yaduwar cutar ta ragu ainun a kasar ta Sin in ban da wasu sassa na kasar.

Wang ya ce, yawancin cutar na yaduwa ne ta hanyar jima'i, sai dai kuma ya ce, yaduwar cutar daga uwa zuwa danta da amfani da allurar shan mugayen kwayoyi ba kasafai ake samun yaduwar cutar ba ta wannnan hanyar a kasar Sin.

Wang ya ce, cutar ta fi shafar dalibai da masu matsakaicin shekaru da kuma wadanda suka manyanta.

Wang ya ce, an kafa cibiyoyi na shan maganin cutar 3, 413 a gundumomi 31 a cikin kasar Sin, kana kuma da cibiyoyi na gwajin cutar ta AIDS har dubu 9 a daukacin kasar ta Sin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China