Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, da takwararnsa na Rwanda Paul Kagame da na Kenya Uhuru Kenyatta sun amince da wannan mataki a lokacin wani taro da suka gudanar, cewar za'a shimfida bututun man ne daga rijiyoyin mai da ke yammacin Ugandan har zuwa tashar ruwa ta Tanga dake Tanzanian.
Sakamakon tattaunawar tasu ya nuna cewar kasashen sun amince a gudanar da wannan aiki.
Kuma sun amince da matakin ne a lokacin taron koli karo na 13 da nufin tattauna hanyoyin da za'a bunkasa cigaban tattalin arzikin yankunan cikin hanzari.
Bugu da kari, taron ya samu halartar jami'an gwamnatocin kasashen Tanzania, da Burundi da Sudan ta kudu.
A halin da ake ciki kasar Uganda, ta fara yunkuri na samar da gangar danyen mai biliyan 6 da digo 5 da aka gano a kasar, kuma tana shirin tace man tare da tura wadanda ba a tace ba zuwa tashar ruwan da ke gabashin Afrika domin a fitar da su zuwa ketare. Ahmad