Wang Yi ya bayyana cewa, hadin gwiwa tsakanin kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan, da kuma Koriya ta Kudu ya riga ya kasance daya daga cikin tsare tsare mafiya samun bunkasuwa a fannin hadin gwiwa a yankin gabashin Asiya, wanda ya taka muhimmiyar rawa a fannin siyasa, da tattalin arziki na Asiya har ma da duniya baki daya.(Fatima)