in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Hua Wei ya taimakawa Senegal wajen horar da gwanaye a fannin sadarwa
2016-06-21 11:11:52 cri
A jiya Litinin 20 ga wata, an kaddamar da bikin sa hannu kan wata yarjejeniya a birnin Dakar, hedkwatar kasar Senegal bisa jagorancin kamfanin Huawei. Bisa yarjejeniyar, kamfanin Huawei zai bayar da wani shirin na tsawon shekaru 3 ga ma'aikatar tarbiya a matsayin koli ta Senegal, a kowace shekara kuma, kamfanin zai ba da kudin agaji ga daliban jami'o'i 10 a wurin domin samun horaswa a Sin. Wannan ne karo na farko da aka gudanar da wannan shiri a Senegal.

Jakadan Sin a Senegal Zhang Xun, da ministan tarbiya a matsayin koli na Senegal Mary Teuw Niane, da babban manajan kamfanin Huawei a Senegal Yu Yong sun halarci wannan biki.

Mr. Mary Teuw Niane ya bayyana cewa, bunkasuwar fasahohin sadarwa na da muhimmanci sosai ga wata kasa wajen samun ci gaban kimiyya da fasaha da tattalin arziki. Kamfanonin Sin suna da fasahohi na zamani a wannan fanni. Rattaba hannu kan yarjejeniyar zai samar da wani zarafi ga daliban jami'o'in Senegal wajen samun fahimtar matasan Asiya da na Turai. A sa'i daya, za su sami horaswa mai kyau, tare da koyon fasahohin sadarwa na zamani.

A shekarar 2008, kamfanin Huawei ya soma kaddamar da shirin, daliban jami'o'i da za su shiga wannan aiki, shekarunsu za su kai daga 18 zuwa 25 da haihuwa, yayin da suke koyon ilmin fasahohin sadarwa a jami'a. Kawo yanzu, an riga an gudanar da shirin a kasashe 67, kamarsu Birtaniya, Faransa, Jamus, Spain da sauransu, yayin da dalibai sama da 1700 suka ci gajiyar aikin.(fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China