in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-11-10 20:43:44 cri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Donald Trump murnar lashe zaben shugabancin Amurka, yana mai fatan karfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin sassan biyu. Hakan dai na zuwa ne a gabar da masu fashin baki ke tofa albarkacin bakin su, game da salon huldar da Mr. Trump zai gudanar da Najeriyar da ma sauran kasashen nahiyar Afirka. (Daily Trust)

Shahararren masanin adabin nan dan Najeriya, wanda ya lashe lambar yabo ta Nobel a shekarar 1986 Farfesa Wole Soyinka, ya yi kurarin yaga takardar shaidar sa ta zama dan Amurka, muddin Donald Trump ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugabancin Amurka a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2017 mai zuwa.

A makon da ya gabata ne dai Soyinka, ya yi wannan kurari yana mai nuna bacin ran sa da yadda Mr. Trump din ya samu takara a babban zaben na Amurka. (The Punch)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China