in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 14 a jihar Borno
2016-11-06 12:47:49 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta dakile wani harin kungiyar Boko Haram a ranar Jumm'a kan wata rundunar soja a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, tare da kashe mayakan kungiyar 14, in ji kakakin rundunar a ranar Asabar.

Kungiyar Boko Haram ta kaddamar da wani hari kan wata bataliya ta 119 ta rundunar sojojin Najeriya dake yankin Malam Fatori dake jihar Borno, in ji Sani Usaman, kakakin rundunar.

Haka kuma, sojojin sun kwato wata igwa da bindigogi kirar AK-47 guda bakwai da kuma tarin alburusai masu yawa bayan gumurzun, in ji mista Sani Usaman tare da bayyana cewa sojojin kasar sun kara zafafa cigaba da aikin kakkabe yankin.

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da ayyukan soja da dama a tsawon 'yan watannin baya bayan nan domin kawar da kungiyar Boko Haram a yankin jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China