in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimman labarai daga wasu jaridun Najeriya
2016-11-17 21:06:08 cri
Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa, duk da kokarin da gwamnatin tarayyar kasar ke yi na tattaunawa da jagororin yankin Niger Delta, har yanzu kungiyoyin tsagerun yankin ba su dauko hanyoyin kawo karshen rikicin da ke faruwa a yankunan da ke da arzikin mai a kasar ba.

Gwamnati ta ce, yadda tsagerun yankin ke ci gaba da barnata bututun mai yana kawo cikas ga tattaunawar zaman lafiyar da ke gudana tsakanin bangarorin biyu.(The Punch)

Har yanzu dai fadar shugaban Najeriya tana ci gaba da zargin gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan da aikata cin hanci, tana mai cewa,tsohuwar gwamnatin ta bayar da kwangilolin karya.(Vangaurd)

A jiya Laraba harkokin karatu sun gurgunce a jami'o'in Najeriya,bayan da malaman jami'o'in kasar suka fara wani yajin aikin gargadi.

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta ce, da farko malaman za su shiga yajin aiki na mako guda, kana za su ci gaba da yajin aiki har sai baba ta gani,idan har gwamnati ta gaza cika alkawarin da suka yi da ita a shekarar 2009, wadanda suka shafi inganta jin dadin malaman da kuma yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin a shekarar 2013 game da gyare-gyaren da suka shafi jami'o'in kasar.(The Guardian)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China