Haka zalika, hukumar ta tabbatar da cewa shirin kasar na dogon zango da rage darajar kudin kasar ba lallai ne ya tabbatar da bunkasuwar zuba jari a kasar ba.
A cewar hukumar kididdigar ta Fitch, sauyawar alkaluman tattalin arzikin kasar daga makoma mai kyau zuwa mummunar makoma, ya faru ne sakamakon rashin tabbas game da tsarin gudanarwar kasar a halin yanzu, kuma wannan matsalar za ta iya ci gaba da shafar tattalin arzikin kasar har zuwa lokacin babban taron zaben shugabannin jam'iyyar ANC mai mulkin kasar a watan Disambar 2017.
A baya bayan nan dai, tattalin arzikin Afrika ta kudun ya fara farfadowa daga matsalolin da sha fuskanta, amma har yanzu akwai rashin tabbas game da makomar kasuwanci da fannin zuba jari a kasar. (Ahmad Fagam)