Ministan shari'a da gyara halayen 'yan kasa Micheal Masutha ya ce, an dauki wannan mataki ne, sakamakon kalaman nuna wariya da wasu abubuwan nuna kyama da ke faruwa a baya-bayan a kasar, don magance irin abubuwan da suka faru a zamanin nuna wariyar launin fata.
Ministan ya shaidawa taron manema labarai a birnin Pretoria cewa, a makon da ya gabata ne majalisar zartaswar kasar ta amince jama'a su tofa albarkacin bakinsu game da dokar, lamarin da ya haifar da kalaman nuna kyama. Wannan ya sa aka bullo da matakan magance wadannan matsaloli tun kafin abubuwa su dagule. (Ibrahim)