Afrika ta Kudu: An fitar da wani rahoto kan "Fahimtar kasa"
Wani rahoton da ake jiransa sosai kan dangantakar da ba ta dace ba da sabawa akida tsakanin shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma da iyalin Gupta na kasar Indiya an fitar da shi a ranar Laraba. Wannan labari ya biyo bayan janyewar wata bukatar mista Zuma zuwa babban kotun kolin Pretoria domin ta hana fitar da wannan rahoto, da wata tsohuwar mai rajin kare moriyar jama'a (Public Protector) madam Thuli Madonsela. Wannan rahoto na samar da bayanai masu tushe dake nuna cewa akwai yiyuwar iyalin Gupta ta kawo tasiri wajen nadin ministoci da wasu manyan shugabannin kamfanonin gwamnati. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku