in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zuma: Sin abokiya ce da ta cika alkawarinta yadda ya kamata
2016-11-08 10:07:50 cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, a shekaru fiye da 50 da suka gabata, Sin tana samar da gudunmawa ga kasarsa, kasancewar kasashen biyu suna sada zumunci da juna. Ya nuna yabo ga kasar Sin domin tana cika alkawurranta yadda ya kamata, kuma ya ce, Sin abokiya ce da ake iya amincewa da ita.

Zuma ya bayyana hakan ne a wajen bikin raba kyautar na'urar komfuta ga makarantar firamare ta Marhulana da aka gudanar a ofishin jakadancin Sin dake kasar Afirka ta Kudu. Kana yana fatan dukkan daliban makarantar ba za su manta ba cewa, Sin tana ci gaba da taimakawa kasar Afirka ta Kudu wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da kimiyya da fasaha, da nuna goyon baya ga gwamnatin kasar wajen gudanar da harkokin kasar yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China