Jiya Alhamis mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao ya bayyana cewa, yankin kahon Afirka wanda ya kunshi kasashen yankin arewa maso gabashin nahiyar, yanki mai muhimmanci a nahiyar Afirka. A saboda haka, samar da zaman lafiya a wannan yanki yana da matukar muhimmanci ga tabbatar da moriyar kasashen dake wannan yanki. Wannan ya sa, kasar Sin take fatan kasashen za su ciyar da hadin gwiwar dake tsakninsu gaba, a kokarin da ake yi na warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari yadda ya kamata.
A jiya ne, aka kada kuri'u kan ko za a tsawaita takunkumin da aka kakabawa kasashen Somaliya da Eritrea, inda aka zartas da kudurin tare da samun kuri'un amincewa guda 10, yayin da mambobi guda biyar ba su jefa kuri'un ba, ciki har da kasar Sin. (Maryam)