Gwamnatin Galmudug, da ta Puntland a Somaliya, suna gaba da juna cikin dogon lokaci. A ranar 28 ga watan Satumban bana, jirgin saman yakin Amurka maras matuki ya kai hari kan wani sansanin soja na gwamnatin Galmudug, wanda ya haddasa mutuwar sojoji masu yawa. Gwamnatin Galmudug, ta zargi gwamnatin Puntland da samar da bayanan sirri masara sahihanci ga sojojin Amurka, shi ya sa sojojin Amurka suka dauki sansanin sojan Galmudug a matsayin sansani ne na kungiyar Al-Shabaab. Kuma Gwamnatin Galmudug ta furta cewa, watakila gwamnatin Puntland ta yi haka ne da gangan.
Sakamakon haka, a ranar 7 ga watan Oktoban bana, sojojin gwamnatocin biyu suka yi musayar wuta tsakaninsu, daga bisani, ko da yake sun daddale yarjejeniyar tsagaita bude wuta, amma ana ci gaba da tarzoma a kai a kai. A ranar 6 ga watan Nuwamban, an sake yin rikici mai tsanani a tsakaninsu, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 20. Bangarorin biyu suna share fagen yin shawarwari kan gudanar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakaninsu a ranar 20 ga wannan wata.(Fatima)