Kwanan nan, wata shahararriyar hukumar binciken ra'ayin jama'a ta Afirka ta wallafa wani rahoto game da yadda al'ummar Afirka suke kallon kasar Sin, inda ta yi bincike tare da kimanta tasirin da kasar Sin ke yi a nahiyar Afirka da kuma yadda al'ummar nahiyar ta Afirka ke kallon kasar Sin. Sa'an nan a jiya Litinin, hukumar ta walafa wani bayani a kan shafinta na Intanet mai lakabin "'yan Afirka na maraba da kasar Sin" domin bayyana sakamakon binciken.
Binciken ya nuna cewa, kasar Sin na ta taka muhimmiyar rawa a Afirka, kuma tana da kima kwarai da gaske a idanun jama'ar Afirka. Aikin zuba jari da sauran harkokin tattalin arziki da ta ke gudanarwa a nahiyar, sun kasance muhimman dalilan da suka kara kimar kasar ta Sin a idon al'ummar nahiyar ta Afirka. Jama'ar da tuntuba da yawansu ya zarce kashi 67 cikin dari na ganin cewa, kasar Sin tana yin muhimmin tasiri a Afirka ta hanyar gudanar da ayyukan tattalin arziki.
Bugu da kari, al'ummar nahiyar Afirka sun yi maraba da taimakon da kasar Sin take bayarwa a nahiyar Afirka domin taimakawa bunkasuwarta. Binciken ya kuma nuna cewa, al'ummar Afirka sun amince da salon ci gaban kasar Sin.(Kande Gao)