in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar masana'antu ya fi jawo hankali ga rage talauci da samun bunkasuwa tsakanin Sin da kasashen Afirka
2016-09-20 20:32:54 cri

A yau Talata ne mataimakin darekta a ofishin kula da harkokin saukaka fatara na majalisar gudanarwar kasar Sin Hong Tianyun, ya bayyana cewa, Sin na fatan hada gwiwa da jama'ar kasashen Afirka kimanin biliyan 1.1, domin jin dadin fasahohin da take da su wajen rage talauci, da na samun bunkasuwa, ta yadda za a tabbatar da makomar bangarorin biyu ta bai daya ta ci gaba da rashin samun talauci.

A yau din nan dai a birnin Shanghai, aka kaddamar da taron rage talauci da samun ci gaba, na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, taron da ke da taken "Yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin masana'antu da rage talauci".

Yayin da yake jawabi a gun bikin bude taron, Hong Yuntian, ya gabatar da matakan da Sin za ta dauka, don cimma burin fitar da masu fama da talauci daga halin da suke ciki nan da shekara ta 2020 bisa tsarin da ake bi a yanzu, yana mai cewa a yayin da take kokarin kawar da talauci a sassan kasar, Sin na dora muhimmanci kan hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa ta fannin saukaka fatara, musamman kasashen Afirka.

A nasa jawabi, jagoran shirin samar da ci gaba na MDD ko UNDP a kasashen Afirka Babacar Cisse, cewa ya yi hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin masana'antu, wani muhimmin mataki ne na cimma burin rage talauci. Ya ce kamata ya yi kasashen Afirka su karfafa hadin gwiwar su da Sin, su kuma koyi darasi daga kasar ta Sin wajen daukar matakan rage talauci bisa hakikanin yanayin da suke ciki.

Jami'an gwamnatoci, da masana, da wakilan kamfanoni da na kafofin yada labarai kimanin 150 daga Sin da kasashen Afirka 15, ciki hadda Mauritius, da Afirka ta Kudu, da Nijeriya, da Mozambique, da Togo da dai sauransu ne, suka halarci wannan taro. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China