A cikin sakonsa, Xi Jinping ya ce, idan aka yi hangen nesa na nan gaba, akwai imani da kyakkyawar makomar hulda tsakanin kasashen Sin da Masar. Mr. Xi ya ce, yana fatan hada kai da Al-Sisi a kokarin zurfafa huldar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu, bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, domin kawo alheri ga kasashen biyu, da al'ummominsu baki daya.
A nasa bangaren, Mr. Abdel Fattah al Sisi ya bayyana cewa, an daga matsayin huldar hadin gwiwa tsakanin Masar da Sin zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, matakin da ya alamta cewa, shugabanni da kuma al'ummomin kasashen biyu suna cigaba da daukar matakai na bunkasa huldar hadin gwiwa tsakaninsu, da nufin sada al'ummun su da moriya, da kuma cimma buri na neman samun ci gaba ba tare da tangarda ba. (Sanusi Chen)