Game da irin wadannan zarge-zargen da gwamnatin kasar Amurka ta yi wa kasar Sin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Alhamis a nan birnin Beijing cewa, matsaya biyu kan dakile ayyukan ta'addanci da wata kasa ta dade tana bi, muhimmin dalili ne dake sanyawa duk da ana namijin kokarin dakile ayyukan ta'addanci a 'yan shekarun nan, har yanzu ba a iya kawar da wannan matsala kwata kwata a duk fadin duniya ba. Ta ce irin wannan matsayi da ake dauka ba zai taimakawa hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasa da kasa wajen dakile ayyukan ta'addanci ba.
Madam Hua ta ce "Kungiyar Turkistan ta gabas ta Musulunci" kungiyar ta'addanci ta kasa da kasa ce da kasashen duniya, ciki har da kasar Sin da kasar Amurka da MDD suka tabbatar. Don haka dakile masu nuna ra'ayin ta'addanci na Turkistan ta Gabas, muhimmin batu ne da kasar Sin ta fi mai da hankali wajen aiwatar da shi. Kaza lika kasar Sin tana fatan kowace kasa za ta mutunta abin da kasar Sin take mai da hankali a kai. (Sanusi Chen)