Mr. Wang Yi ya jaddada babbar ka'idar da kasar Sin take bi wajen batutuwan da suke shafar jihar Tibet, kuma ya nemi bangaren Amurka da ya daina tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin, kuma ya dauki matakan a zo a gani wajen kare dangantakar dake kasancewa tsakanin kasashen Sin da Amurka.
A nasa bangaren, John Kerry ya bayyana cewa, bangaren Amurka bai canja manufofinsa game da yankin Tibet ba, kuma ba za a canja su ba. A ganin bangaren Amurka, yankin Tibet wani yanki ne da ba za a iya raba shi daga kasar Sin ba, bangaren Amurka ba zai nuna goyon baya ga yunkurin 'yancin Tibet ba. (Sanusi Chen)