Rahotanni na cewa, kamfanoni guda 8 na kasar Sin, ciki har da gidan rediyon kasar Sin CRI, da sashen shirya hotunan bidiyo na gidan talabijin na kasar Sin CCTV wato CCTV+, da kuma kamfanin Star Times da sauransu sun halarci bikin. Abubuwan da aka nuna a yayin bikin sun shafi wasannin kwaikwayon talabijin, shirye-shiryen bincike, wasannin ban dariya da kuma shirye-shiryen nishadantarwa.
Wani jami'in kamfanin Star Times ya bayyana cewa, yanzu haka an fassara wasu wasannin kwaikwayon kasar Sin daga harshen Sinanci zuwa harsunan Turanci, Faransanci, harshen Swahili, harshen Hausa, harshen Yoruba da dai sauransu, don watsa su a kasashen Afirka. Kuwa wadanda suka fi samun karbuwa a wajen al'ummar Afirka su ne wasannin kwaikwayo game da Kongfu, da wasu da suka shafi rayuwar matasa da kuma bayyana yadda Sinawa ke rayuwa a kasashen Afirka, ko yadda 'yan kasashen Afirka ke rayuwa a kasar Sin. (Bilkisu)