Shigar Masar a cikin kwamitin kare hakkin dan adam na MDD na shaida wani muhimmin matsayinta da karfafa karbuwarta a cikin gamayyar kasa da kasa, in ji Ahmed Abu Zeid, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.
Zaben a cikin kwamitin kare hakkin dan adam ya kasance wata alama ta cewa, Masar tana taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tsaro da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya da kuma Afrika, har ma da karfafa ka'idojin 'yancin kasa da kasa da girmama kundin tsarin MDD, a cewar wannan sanarwa.
An zabi Masar a ranar Jumma'a bisa wa'adin shekaru uku tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2017. Wannan yana bayyana wata sabuwar nasarar diplomasiyya da tabbatarwa na amincewa kasa da kasa game da wannan kasar Larabawa, in ji kakakin.
Haka kuma ya bayyana farin cikin Masar game da dukkan kasashen da suka nuna mata goyon baya wajen zabenta. A tsawon wannan sabon wa'adi, kasar Masar za ta jajirce wajen kara karfafa karfin kwamitin a cikin aikinsa na bunkasa da kare 'yancin dan adam, in ji mista Abu Zeid. (Maman Ada)