A ranar Jumma'a 14 ga wata, an kai hari kan wata tashar bincike ta rundunar sojan Masar a jihar Sinai ta arewa, wanda ya haddasa mutuwar sojoji 12, yayin da wasu sojoji 6 suka ji rauni. Kana wasu dakaru 15 suka mutu a cikin musayar wuta.
A daren ranar 14 ga wata, reshen kungiyar IS a jihar Sinai ta arewa ya ba da sanarwa a shafinsa na yanar gizo cewa, inda ta yi shelar daukar alhakin kai wannan hari.
Bayan harin, shugaban Masar Abdul Fatah Al-Sisi ya ba da sanarwar, inda ya mika ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, tare da nuna cewa, wannan hari zai karfafa niyyar kasar wajen yaki da ta'addanci.(Fatima)




