in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta yi allawadai da harin ta'addanci a yankin Sinai na kasar Masar
2016-10-16 13:58:52 cri
Kasar Sudan ta yi allawadai a ranar Asabar da harin ta'addancin da aka kai a ranar Jumma'a wanda ya kashe sojojin Masar 12 a yankin arewacin Sinai na kasar Masar.

Gwamnatin Sudan ta yi alladawai da babbar murya kan harin ta'addancin da ya faru a yankin arewacin Sinai na Masar, wanda ya halaka sojojin Masar da dama da kuma fafaren hula da ba su ji ba su gani ba, in ji ma'aikatar harkokin wajen Sudan a cikin wata sanarwa.

Ma'aikatar ta bayyana wannan harin a matsayin wani babban laifi da ya sabawa dukkan daraja da ka'idojin jin kai. Haka kuma ta isar da juyayinta ga iyalin mamatan, da kawo goyon bayan Sudan ga kasar Masar ta yadda zata dauki matakan da suka dace domin kare jama'arta gaban hare haren ta'addanci da ayyukan manyan laifuffuka.

A cewar majiyoyin tsaron Masar, sojoji 12 suka mutu a ranar Jumma'a kana 6 suka jikkata a wani harin da aka kai a wata tashar binciken tsaro mai nisan kilomita 85 daga yammacin Al Arish, babban birnin gundumar Sinai. Reshen kungiyar IS dake Sinai ya dauki alhakin kai wannan hari. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China