A ranar Litinin ne, kasar Masar ta janye yiyuwar kafa sansanonin sojojin kasashen waje a kasarta, in ji kafar gwamnatin kasar Al-Ahram bisa shafinta na internet.
A cewar Kafar Al-Ahram, kakakin fadar shugaban kasar Masar ya yi watsi da labaran baya bayan nan dake kafofin kasar dake bayyana cewa akwai alamar hukumomin Moscow na shawarwari tare da hukumomin Alkahira kan batun gina wani sansanin soja kusa da tekun Bahar Rum.
A cewar mujallar Rasha Izvestia, kasar Rasha na kan hanyar tattaunawa tare da Masar bisa burin hayar wani adadin sansanonin soja wanda ta hada wani sansanin sojojin sama a birnin Sidi Barani, mai tazarar kilomita 95 daga gabashin iyaka tsakanin Masar da Libiya, wannan kuma tun daga shekarar 2019.
Wata majiyar soja ta tabbatarwa Al-Ahram cewa, Alkahira ta yi watsi kwata kwata da bukatun wasu kasashe na gina sansanonin soja a Masar, tare da bayyana cewa sansanonin sojan kasashen waje suna sabawa ka'idojin gwamnati.
Masar da Rasha, a shekarun baya suna gudanar huldar dangantaka mai kyau a cikin shekarun 1960 har zuwa karshen shekarun 1970, sun maido huldar soja da siyasa mai karfi tun bayan kama ikon shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi a shekarar 2014.
A shekarar da ta gabata, jiragen ruwan yakin kasashen biyu sun shirya atisayen sojansu na farko cikin hadin gwiwa a gabar birnin Alexandiriya na Bahar Rum, bisa tsawon kwanaki takwas. (Maman Ada)