Mataimakin ministan kudin kasar Sin mista Dai Baihua ne ya jagoranci tawagar kasar Sin wajen halartar taron. A jawabin da ya gabatar, Mr. Dai ya bayyana cewa, yankin Asiya da tekun Pasifik ya kasance daya daga cikin yankunan da ke samun ci gaban tattalin arziki mafi sauri a duniya. A ganinsa, nan gaba, ya kamata a daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin kasashen Asiya da tekun Pasifik, don neman karuwar tattalin arzikin mai dorewa wanda zai amfani kowa.
Ban da haka kuma, ya kamata a inganta hadin gwiwar kasashen dake yankin a fannonin zirga-zirga, da sadarwa, da harkar kudi, da mu'ammalar al'umma, da dai sauransu. Kaza lika a kyautata muhallin zuba jari, da daidaita matsalar koma bayan kayayyakin more rayuwa, da dai makamantansu, don kara ciyar da tattalin arzikin yankin gaba. (Bello Wang)