in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron hadin gwiwar tattalin arzikin APEC 2016 a Peru
2016-11-15 09:43:37 cri

An bude taron hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen Asiya da yankin Fasifik APEC na shekarar 2016 a birnin Lima na kasar Peru, taron da aka yiwa lakabi da "ci gaba mai nagarta da bunkasar rayuwar bil Adama."

Rahotanni sun bayyana cewa, mahalarta taron da suka kunshi shugabanni, da manyan jami'ai, da 'yan kasuwa daga kasashe mambobin kungiyar APEC 21, za su tattauna tsakanin ranekun 14 zuwa 20 ga watan nan, game da makomar huldodin cinikayya, da ci gaban tattalin arziki, tare da hanyoyin inganta rayuwar al'umma.

Ana sa ran shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai jagoranci taron shugabannin na APEC game da tattalin arziki, wanda zai mai da hankali ga hanyoyin bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen yankuna. Kaza lika shugaba Xi zai gabatar da jawabi a yayin wannan taron.

Kasar Sin ta shafe shekaru 25 tana ba da gudunmawa ga APEC, a wani mataki na raya ci gaban kasashen Asiya da yankin Fasifik. Ana sa ran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Barack Obama za su halarci wannan taro.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China