in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya ta yi kira ga kasashen duniya ba da muhimmanci game da batun Mali
2016-05-16 10:11:58 cri
Ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Ramtane Lamamra ya yi kira ga kasashen duniya da su kara ba da muhimmanci game da batun kasar Mali, don taimaka wa bangarorin kasar da rikicin ya shafa da su aiwatar da yarjejeniyar samar da zaman lafiya da samun sulhuntawa da aka cimma.

Ramtane wanda ya yi wannan kira a jiya, ya kuma fada wa kamfanin dillanci labarun kasar Aljeriya cewa, kasar ta dora muhimmanci sosai game da yunkurin sulhunta bangarorin daban daban da rikicin Mali ya shafa, kuma kullum tana kokari ba dare ba rana don ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Mali da ma yankin Sahele baki daya. Ya jaddada cewa, Aljeriya ta taka rawar shiga tsakani game da rikicin kasar Mali, don kara amincewa da juna tsakanin bangarorin daban daban na kasar Mali, a kokarin aza wani harsashi don daddale yarjejeniyar samar da zaman lafiya da samun sulhuntawa.

Ya ce, a cikin shekarar da ta gabata, kokarin kasar Mali ya samu babban ci gaba, amma duk da haka ana fuskantar wahalhalu da dama, sabo da haka, ya yi kira ga kasashen duniya da su inganta hadin gwiwa, don sa kaimi ga aiwatar da yarjejeniyar samar da zaman lafiya yadda ya kamata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China