in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeriya ta karyata zargin da rahoton Amurka ya yi mata game da safarar bil adama
2016-07-18 10:54:07 cri
Ministan shari'a na kasar Algeriya ya musanta rohoton da Amurka ta fitar game da zargin kasar da aikata laifukan safarar bil adama.

MinistaTayeb Louh, ya dage cewar babu kamshin gaskiya game da zargin da rahoton ke yiwa kasar game da alaka da safarar bil adama, kuma tuni kasar ta gabatar da rahotonta na shekara shekara ga MDD da ya shafi dukkan batutuwan kasar, ciki har da batun na safarar bil adama.

Ya kara da cewar, dokokin kasar Algeriya sun tanadi hukunci ga dukkan wadanda aka kama da hannu wajen aikata laifukan safarar bila adama, kuma jami'an tsaron kasar na ci gaba da gudanar da ayyukansu, kuma a halin yanzu laifuka 2 ne kachal aka tabbatar da suke da alaka da safarar bil adama a kasar, kuma tuni aka zartar da hukunci ga wadanda ke da hannu a laifukan.

A farkon wannan watan ne rahoton na Amurka, ya bayyana sanya Algeriya cikin kasashe uku da suka yi kaurin suna a duniya wajen aikata laifukan safarar bil adama, musamman wajen bautar da mata da tilasta su yin karuwanci, kana da bautar da maza.

Rahotan dai ya bayyana Algeriya a matsayin wani sansanin bakin haure da masu safarar bil adama, wanda ta kasance matattara ce ga bata gari dake kwarara daga kasashen kudu da hamadar sahara kamar su Nijer, da Chadi. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China