Mai magana da yawun sojin Sudan ta kudun Santo Dominic Chol, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, ana fama da rikice rikice a sassa daban daban na kasar, amma ya musanta ikirarin da dakarun dake biyayya ga Machar suka yi na kwace ikon wasu garuruwa a kasar.
Ya ce a cikin yan makonnin nan, mayakan na SPLM-IO suna cigaba da zafafa hare hare kan yankunan dake karkashin ikon gwamnatin kasar.
A ranar Larabar da ta gabata ne, mai magana da yawun SPLM-IO Dickson Gatluak, ya yi ikirarin cewa dakarunsu sun kwace iko a Bazi, yankin dake kan iyakar Sudan ta kudu da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Morobo a tsakiyar jahar Equatoria, sai kuma Kaljak a jahar hadin kai.