A wata sanarwa daga ofishin babban jami'i mai kula da 'yan gudun hijira na MDD (UNHCR), wadda aka fitar a Juba ta ce, wasu 'yan bindiga dauke da makamai ne suka harbe 'yan gudun hijira 2 da kuma jikkata wasu 5 wadanda suka fito daga yankin Kordofan a Sudan ta kudu.
A cewar ofishin na UNHCR, 'yan bindigar sun saki wasu 'yan gudun hijirar da suka yi garkuwa da su tun a ranar 19 ga watan Oktoba.
Sanarwar ta kara da cewa, har yanzu akwai ragowar mata 4, da kananan yara 28 da aka yi garkuwa da su wadanda ba'a san takamamman inda ake tsare dasu ba, sai dai ana cigaba da kokarin gano yadda ake tsare da su.
A cewar ofishin na UNHCR, masu garkuwar sun saki wasu 'yan gudun hijirar 7 da suke tsare da su a ranar 5 ga wannan watan. Bayan sakin nasu ne, wata kungiyar ta sake afka musu.
Sanarwar ta kara da cewa, an harbe guda daga cikin 'yan gudun hijirar, sannan an ji wa 6 daga cikinsu raunuka. Kafin 'yan gudun hijirar su isa garin Yei, guda daga cikin su ya mutu sakamakon raunukan da aka ji musu. UNHCR ta kwashe 'yan gudun hijirar 5 a jirgin sama zuwa Juba domin a duba lafiyarsu.(Ahmad)