Jami'an hukumar ta bincike da sa'ido (JMEC) wacce ke lura da batun aiwatar da yarjejejniyar zaman lafiya da aka kulla a watan Agastan 2015 sun ce, saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ba abin da za'a amince da shi bane.
Cikin wata sanarwar da jagoran tawagar ta JMEC Festus Mogae ya fitar a Juba yace, sun damu matuka game da yawaitar tashin hankali da take hakkin bil adama da ake cigaba da fuskanta a kasar tun a watan Yuli. Kuma yin watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ba abu ne da za'a lamunce da shi ba.
Mogae wanda tsohon shugaban kasar Botswana ne, kuma shi ne zai jagoranci taron tattaunawar JMEC da za'a gudanar a ranar 19 ga wannan wata.
Ya bukaci bangarorin da yarjejeniyar zaman lafiya ta shafa a kasar, dasu amince da hawa teburin sulhu domin lalibo bakin zaren warware takaddamar siyasar kasar, kuma su nuna halin dattaku kamar yadda al'ummar kasar ke bukata.
Ana saran JMEC zata gabatar da rahotonta a gaban mambobin hukumar, wadan da suka hada da wakilan masu fafutukar kafa gwamnatin hadin kan kasa, da masu ruwa da tsaki a kasar Sudan ta kudu, da mambobin kungiyar (IGAD), da hukumomin kasa da kasa, da kawayen Sudan ta kudu.
Manyan ajandojin taron, sun hada da batun nazari kan rahoton saba yarjejeniyar zaman lafiya, da kafa gwamnatin hadin kan kasa, da batun halin da alumma ke ciki a kasar, sai kuma batun tura dakarun musamman don tabbatar da zama lafiya.