An cafke mutane 17 a Sudan ta Kudu bisa aikata fyade ga ma'aikatan bada agaji
Hukumomin Sudan ta Kudu sun tabbatar a ranar Laraba da kama mutane guda 17, wadanda suka hada da sojoji, bisa laifin aikata fyade ga ma'aikatan jin kai a yayin yake yake tsakanin dakaru masu gaba da juna a cikin watan Yuli. Mataimakin ministan shari'a, Martinson Oturomoi, dake jagorantar kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike kan wannan hadarin, ya bayyana cewa wadanda aka yi wa fyaden da kuma wasu ganau da kwamitin ya yi wa tambayoyi sun tantance gungun mutanen da suke aikaita fyaden ga ma'aikatan jin kai da kuma lalata ginin da wata hukumar agaji take ciki a Juba, babban birnin kasar a ranar 11 ga watan Yuli. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku