Hukumar kula da mutanen da suka kaura zuwa kasashen waje ta duniya ta gabatar da wani sabon rahoto a birnin Geneva cewa, yawancin mutanen da suka mutu suna kokarin ratsa bahar Rum ne daga arewacin nahiyar Afirka zuwa kasar Italiya, kana 420 a cikinsu sun mutu a gabashin bahar Rum a kan hanyarsu daga Turkiya zuwa Girka, da wasu 62 daga cikinsu sun mutu a yammacin bahar.
Bisa kididdigar da aka yi, ya zuwa ranar 18 ga wannan wata, yawan 'yan gudun hijira da bakin haure da suka ratsa bahar Rum zuwa nahiyar Turai a bana ya kai kimanin dubu 343 da dari 6, amma yawansu daga watan Janairu zuwa Oktoba na bara ya kai dubu 729. A ganin kakakin hukumar, wannan jimillar ta shaida cewa, yanzu ana fuskantar karin hadari ne yayin da ake kokarin ratsa bahar Rum zuwa nahiyar Turai. (Zainab)