A lokaci taron wanda aka gudanar a Larabar nan a Addis Ababa, shugaban ICRC, Peter Maurer, ya yiwa majalisar tabbatar da tsaro da zaman lafiya na kungiyar AU karin haske game da ziyarar da ya kai kwanan nan kasashen Najeriya da Nijer, da sauran batutuwa da suka shafi AU da ICRC
Ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan 10 ne ke rayuwa a sansanonin yan gudun hijira a nahiyar Afrika, Maurer ya bukaci kasashen Afrika da su gaggauta amincewa tare da aiwatar da yarjejeniyar domin ba da kariya, da kuma tallafawa mazauna sansanonin yan gudun hijirar.
Ya kara da cewa, daftarin yarjejeniyar ya kunshi matakan da kasashen na Afrika za su bi wajen tallafawa da kuma bada kariya ga mazauna sansanonin yan gudun hijirar, ya ce, "dukkanin kasashen Afrika za su amince da wannan yarjejeniya, kuma kasashen da suka amince da ita zasu aiwatar da dukkan yarjejeniyar. Kungiyar tarayyar Afrika tana da gagarumar rawa da zata taka game da hakan". (Ahmad)