in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a warware matsalar 'yan gudun hijira a dukkan fannoni
2016-10-06 12:44:11 cri

Wakilin dindindin na kasar Sin dake ofishin MDD a Geneva mista Ma Zhaoxu, kana wakilin Sin a sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Swiss ya bayyana ra'ayi da manufar kasar Sin game da batun 'yan gudun hijira.

A yayin da yake yiwa kwamitin zartaswa kan harkokin 'yan gudun hijira na MDD jawabi a yayin babbar muhawarar MDD karo na 67 da aka yi a ranar 4 ga wata, mista Ma ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashe daban daban su kasance masu nuna tausayi, da kara samar da tallafin kudi, domin kare mutunci, tsaro da inganta rayuwar 'yan gudun hijira da dai sauransu.

Baya ga haka, mista Ma ya bayyana cewa, a matsayinta na kasa mai kujerar dindindin a kwamitin sulhun MDD, kana kasa mai tasowa mafi girma a duniya, a kullum kasar Sin na kokarin kiyaye zaman lafiyar duniya, da taimakawa kokarin da ake yi na samu ci gaba tare. Haka kuma Sin na kokari wajen warware muhimman batutuwa a siyasance, tana kuma fatan taka rawa wajen warware matsalar 'yan gudun hijira.

Ma ya kara da cewa, kasar Sin tana son ci gaba da samar da taimakon jin kai ga wasu kasashe da kungiyoyin kasa da kasa, da karfafa hadin kai tare da hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira, da kuma yin kokari tare da kasashe daban daban domin inganta ayyukan kiyaye 'yan gudun hijira na duniya, da nufin hanzarta warware wannan batu yadda ya kamata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China