A wannan rana hukumar UNHCR ta ba da sanarwa a birnin Kampala cewa, 'yan gudun hijira na Burundi sun gudu zuwa Tanzaniya da Ruwanda da Uganda da Kongo Kinshasa da kuma Zambiya sakamakon barkewar tashe tashen hankali, barazana, yin garkuwa da sace mutane da sauransu.
Hukumar ta bayyana cewa, sabo da karancin karfi na wasu kasashen dake karbar 'yan gudun hijira, 'yan gudun hijira na Burundi da dama, musamman ma mata da yara, suna cikin mawuyacin hali.
Sanarwar ta kara da cewa, domin ba da kariya ga 'yan gudun hijira, hukumar UNHCR ta yi kira ga kasa da kasa da su yi kokarin tabbatar da zaman lafiya, tare da kara nuna goyon baya ga wadannan kasashe masu karbar 'yan gudun hijira.(Fatima)