A cewar wani kudurin da aka cimma da kuri'u 19 na amincewa da kuri'u 7 na kin amincewa kana da kuri'in janye jiki 21, wannan kwamitin bincike zai kula da tantance mutanen da aka zarge da tauye tauyen hakkin dan adam da aka aikata a cikin kasar, da tsara wasu shawarwari kan matakan da za a dauka domin tabbatar da cewa wadannan mutane sun amsa laifinsu gaban kuliya, duk da matsayin da suke da ko wani goyon baya, da kuma tattaunawa tare da hukumomin Burundi da dukkan bangarori daban daban masu ruwa da tsaki ta yadda da za a samar da tallafi da shawarwarin da suka wajaba wajen kyautata nan take matsalar 'yancin dan adam da kuma yaki da rashin hukunci, in ji MDD a cikin wata sanarwa.
Haka kuma,kwamitin 'yancin dan adam din ya bukaci gwamnatin Burundi da ta bada hadin kai yadda ya kamata ga kwamitin binciken, da bada umurnin kai ziyara a cikin kasar da kuma samar da dukkan bayanan da ake bukata wajen tafiyar da aikin tawagar binciken, in ji sanarwar. (Maman Ada)