Sanarwar ta zo ne bayan wata ziyarar da jami'an ICGLR suka kaiwa sabon babban sakataren shugaba Pierre Nkurunziza na kasar Burundi, Zachary Muburi Muita.
Dangantaka ta fara tsami ne tsakanin kasashen Burundi da Rwanda, tun a watan Afrilun shekarar 2015, a lokacin da shugaban kasar Burundin Pierre Nkurunziza, ya yanke shawarar neman wa'adin shugabancin kasar a karo na 3, lamarin da ya saba da dokokin kundin tsarin mulkin kasar, da kuma batun yarjejeniyar Arusha ta 2000.
An zargi kasar Rwanda da laifin ba da mafaka ga 'yan kasar Burundi wadanda suka yi yunkurin shirya juyin mulki a ranar 13 ga watan Mayun shekarar 2015, sannan an zarge ta da ba da horo na soji ga wasu mutane da nufin ta da hankalin kasar Burundin.
Sai dai Rwanda ta sha musanta zarge zargen da ake yi mata. (Ahmad Fagam)