in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO ta bukaci a tinkari sauyin yanayin duniya ta hanyar bunkasa aikin gona
2016-10-15 12:10:49 cri
A jiya Jumma'a, hukumar kula da harkokin aikin gona da samar da abinci ta duniya wato FAO, ta bukaci kasashen duniya da su yi kokari tare kan yadda za a tinkari sauyin yanayin duniya da matsalar karancin abinci, da radadin talauci, ta hanyar rungumar salon bunkasa aikin gona na zamani, domin cimma burin neman samun dawaumammen ci gaba.

A wannan rana, hukumar FAO ta shirya wani biki a birnin Rome na kasar Italiya a jajibiren "Ranar abinci ta duniya karo na 36". Babban jigon "ranar abinci ta duniya" na shekarar bana shi ne "halin da ake ciki ta fuskar abinci da aikin gona da kuma sauye-sauyen yanayin da duniya ke fuskanta".

A yayin bikin murnar "ranar abinci ta duniya karo na 36", Mr. Jose Graziano da Silva, babban direktan hukumar FAO ya bayyana cewa, a cikin "yarjejeniyar Paris" da ajandar neman dawaumammen ci gaba nan da shekarar 2030 da kasashen duniya suka kulla, sun amince cewa, bunkasa dawaumammen aikin gona zai taka rawa mafi muhimmanci ga kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya da kawar da yunwa da talauci. Sakamakon haka, ana bukatar karin fasahohin zamani, da ilmi, da kasuwanci, da samar da kudade domin tallafawa wajen aiwatar da shirin yadda ya kamata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China