An dai gudanar da taron ne a jiya Laraba 11 ga wata a birnin Rome da ke kasar Italiya. Yayin zaman, Da Silva ya ce, kawar da yunwa da talauci a duniya, ya zama babbar gudummawa ta samar da dauwamammen zaman lafiya. A sa'i daya kuma, aikin gona da samar da isasshen abinci, zai taimaka wa iyalai da yankunan da rikici ya shafa. (Bako)