in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO: Kasashe da dama na bukatar tallafin abinci sakamakon yanayin El-Nino da rikice-rikice
2016-06-03 10:14:16 cri
A jiya Alhamis ne, kungiyar kula da abinci da aikin gona ta M.D.D. wato FAO ta fidda wani sabon rahoto game da matsalar abinci da za a fuskanta, inda aka bayyana cewa, sakamakon yanayin El-Nino da yaki-ci-yaki-cinyewa, yanzu, kasashen da ke bukatar tallafin abinci ya karu daga 34 a watan Maris zuwa 37.

Rahoton ya nuna cewa,matsalar ta El-Nino ta haifar da mummunan tasiri a kasashen da ke yankunan Fasific da Caribbean, wanda ya haifar da karancin abinci, da karuwar mutanen da ke fama da yunwa, kana yanayin rashin samun isasshen abinci ya kara kamari. A kasashen da ke yankunan kudancin Amurka da kudancin Afrika kuwa, matsalar El-Nino ta yi mummunar illa. Ban da wannan kuma, a cikin kasashe 28 da kungiyar FAO ta gudanar da binciken ta, yanayin samar da abinci ya yi kamari a cikin kasashe 12 daga cikinsu, sakamakon rikici.

A wani bangare kuma, rikicin da ya ci gaba da tsanata a yankin arewacin kasar Nijeriya, ya haddasa mutane da dama barin gidajensu, abun da ya sa kasashe makwabta kamarsu Kamaru, Chadi, da Nijer, da sauransu, suka kara samun 'yan gudun hijira da dama, kuma ba a iya tabbatar da samun isassun abinci a wadannan kasashe. Sabo da haka, duk da cewa, Nijeriya a matsayinta na kasar da ke karfin tattalin arziki a Afrika, wadda ke da yawan al'umma a nahiyar, amma an sake sanya sunanta cikin jerin kasashen da ke bukatar tallafin abinci daga kasashen waje.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China