Shugaban kasar Argentina Mauricio Macri da takwaransa na Uruguay Tabare Vazquez, suka sanar da hakan, bayan wata tattaunawar da shugabannin biyu suka gudanar a Buenos Aires.
A cewar Macri "za mu yi aiki tare, da nufin shiryawa tare da karbar bakuncin gasar wasannin kwallon kafa ta duniya a shekarar 2030.
Vazquez ya jaddada tasirin da zakarun yan wasan kwallon kafa na kasashen ke yi ga harkar wasannin kwallon kafa ta duniya.
Shugaban na Uruguay yace " ina magana ne kan Leo Messi da Luis Suarez,".
Wasannin na shekarar 2030, zasu tabbatar da cika karni guda da kasar ta Uruguay ta lashe kyautar gasar kwallon kafan ta duniya. Ana saran kwamitin shirya wasannin kwallon kafan ta duniya FIFA, zai yanke kuduri game da baiwa kasashen da zasu karbi bakuncin gasar wasannin kwallon kafan da za'a gudanar a shekarun 2026, da 2030 da kuma 2018.(Ahmad Fagam)