in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa masu sha'awar kwallon kafa na bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da zuwan Lippi
2016-10-26 21:03:02 cri
A ranar Asabar ne aka bayyana sunan koci Marcello Lippi dan asalin kasar Italiya, a matsayin mutum da zai jagoranci babbar kungiyar kwallon kafar kasar Sin, yayin da kungiyar ke fafutukar samun gurbi a gasar cin kofin duniya da kasar Rasha za ta karni bakunci a shekara ta 2018.

Sai dai duk da daukar wannan mataki, wasu Sinawa masu sha'awar kwallon kafa na ganin ganin an makara, ganin cewa tuni aka fara wasannin neman gurbin gasar ta duniya da hukumar FIFA ke shiryawa.

Cikin masu wannan ra'ayi akwai matashi mai suna "Shuineng" wanda ya bayyana ta bakin sa, a daya daga zaurukan mahawara na kasar Sin wato Hupu.

Wani mutumin na daman shima na ganin cewa hukumar kwallon kafar kasar ta (CFA) ta makara, ganin yadda tuni Sin din ta sha kashi a hannun abokanan karawar ta a wasanni 4 da ta buga na neman gurbin. Kasar Sin dai na da maki guda ne kacal, kuma ita ce ke kasan teburin rukunin ta na kasashe 6, wadanda suka hada da Korea ta Kudu, da Iran, da Uzbekistan, da Qatar da kuma Syria.

Bisa tsarin wasannin na neman gurbi, kasashe biyu dake saman teburin ne za su wakilci rukunin, zuwa gasar cin kofin na duniya a kasar Rasha.

Hukumar CFA dai ta dora hoton Lippi a kan shafin ta na yanar gizo yana murmushi, lokacin da yake sanya hannu kan kwantiragin horas da kungiyar kwallon kafar ta Sin, amma bata fayyace sauran batutuwa da suka shafi kwangilar ba.

Wani masoyin wasan kwallon kafa da ya bayyana ra'ayin sa game da hakan mai lakabin "netizen", ya ce "Zai dau kasar Sin dan lokaci kafin ta zama zakara a fannin kwallon kafa a nahiyar Asiya. Ina fatan 'yan kallo da mahukunta za su yi hakurin hakan," Ya kuma kara da cewa "bai dace a kashe makudan kudade wajen hayar babban koci irin wannan ba, saboda kawai ya jagoranci wasanni 6".

A shafin Weibo kuwa, Likui ne ke cewa, "Ina kaunar Lippi! Ina masa fatan alheri a dukkanin rayuwar sa. Ina ga ba ya bukatar nuna wani abu sabo. Mutum ne shi gwarzo kuma jarumi!.

Shi kuwa "Frozen" cewa yake Lippi ya wuce matsayin koci ga kungiyar kwallon kafar Sin. "Wannan mutum dan kasar Italiya ya dace ya zama jakadan kwallon kafar kasar Sin. Za mu amfana matuka daga gare shi sama da matsayin sa na mai horas da 'yan wasa.

Kaza lika "Frozen" ya kara da cewa "Bana jin Lippi zai maimaita kuskuren da Jose Camacho ya yi. Camacho ya jagoranci kungiyar kwallon kafar Sin daga watan Agustar 2011 zuwa watan Yunin 2013, lokacin da ya ajiye aiki, bayan da kasar Thailand ta zurawa kasar Sin kwallaye 5 da 1, a wasan sada zumunta da suka buga ranar 15 ga watan na Yunin 2013.

Kaza lika wadanda suka biyo bayan Camacho wato Fu Bo, da Alain Perrin, da Gao Hongbo suma basu iya sauya yanayin da Sin din ke ciki ba ta fuskar kwallon kafa. A baya bayan nan ne kuma Gao ya ajiye aikin horas da 'yan wasan na Sin, bayan da Uzbekistan ta lashe wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da ta buga da Sin, wasan da aka tashi 2 da nema a ranar 11 ga watan Oktobar nan.

Lippi dai ya taka rawar gani a lokacin da ya jagoranci kungiyar Guangzhou Evergrande dake birnin Guangzhou a nan kasar Sin, tsakanin shekarar 2012 zuwa 2014. Inda ya cimma nasarar lashe kofin kalubale na kasar Sin a kakar wasa ta 2013 tare da kungiyar ta Guangzhou Evergrande. Yana kuma cikin masu horas da 'yan wasa mafiya shahara a duniya.

Wasu masu fashin baki na ganin mai yiwuwa ne Lippi ya bada babbar gudummawa ga kungiyar kwallon kafar kasar Sin, musamman ma bayan da mahukuntan kasar suka fidda babban tsarin sauya alkiblar wasa kwallon kafa na kasar a watan Fabarairun shekarar bara, inda suka fidda wani kuduri na dogon lokaci, da nufin daga martabar harkar kwallon kafar kasar zuwa matsayi mafi daukaka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China