in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar zai iya jagorantar Brazil a gasar kofin duniya; inji Tostao great
2016-10-12 16:45:21 cri
Dan wasan kwallon kafan Brazil great Tostao yayi amanna cewa zakaran wasan Barcelona Neymar zai iya taimakawa yan kungiyar wasa ta Selecao a gasar cin kofin duniya karo na 6 da za'a gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018.

Brazil wacce ta lashe lambar yabo a gasar kwallon kafa ta duniya a 2002, sai dai ta gane kuskurenta a hannun Jamus a gasar shekarar 2014 da ci 7-1 a wasan kusa da na karshe.

To sai dai, Tostao yana ganin an dan samu cigaba karkashin jagorancin kociya na yanzu Tite, wanda ya maye gurbin Dunga a watan Yuni, bayan da kungiyar wasan ta fuskanci lugude daga hannun Copa ta Amurka.

Tostao ya fadawa jaridar Globo cewa; "Brazil tana da damar lashe gasar saboda yawan 'yan wasa masu tsaron gida da muke dasu, gami da Neymar da sauran fitattun 'yan wasa da suke tasowa". "Tasowar kwararrun 'yan wasan, wata alamace dake nuna cewa zamu iya samun mashahuriyar tawagar 'yan wasa a 2018."

Brazil tayi nasarar lashe wasanninta na farko ne karkashin jagorancin Tite, inda ta samu matsayi na biyu a gasar wasannin share fagen cin kofin duniya a rukunin shiyyar kudancin Amurka.

Duk da irin nasarar da tawagar 'yan wasan ta samu, Tostao ya damu matuka game da koma bayan da yan wasan tsakiya na kungiyar wasan ke samu.

Shahararren dan wasan kwallon duniya a shekarun 1970 ya kara da cewa; "An samu Baraka a Brazil har kusan tsawon shekaru 20 a tsakanin 'yan wasan tsakiya da kuma kai hare hare kan 'yan wasan tsakiyar".

"Toni Kroos, bashi da gurbi a kungiyar wasan kwallon kafa ta Brazil, saboda shi ba mai tsaron gida bane, kuma baya iya taka leda a matsayin dan wasan tsakiya. Muna tafiyar hawainiya wajen gano bukatar da muke da ita na irin 'yan wasan tsakiyar da suka fi dacewa, ko da yake, har yanzu muna da matakai da zamu iya daukarsu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China