in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin kamfanin samar da wutar lantarkin kasa ta Sin a ketare ya kai dallar Amurka biliyan 40
2016-11-16 13:59:19 cri
Cikin 'yan shekarun nan, kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya dukufa wajen aiwatar da manufar zuba jari a waje da kuma shirin zirin tattalin arziki na siliki da hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, inda ya yi ta zuba jari a waje yadda ya kamata, yayin da ya ke hadin gwiwa da kamfanonin kasa da kasa a fannin makamashi da kayayyakin wutar lantarki, ta yadda za a karfafa hadin gwiwa da shawarwari a tsakanin kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa a wannan fanni.

Rahotanni na cewa, ya zuwa yanzu kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya yi nasarar zuba jari a kasashe da yankuna guda shida wadanda suka hada da Philippines, Brazil, Portugal, Australia, yankin HongKong na Sin da kuma Italiya. Haka kuma, ayyukan da kamfanin ya yi ba kawai sun shafi kasashe masu tasowa ba, har ma da kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki da kuma kasashe masu ci gaba.

Bugu da kari, adadin jarin da kamfanin ya zuba a ketare ya kai sama da dallar Amurka biliyan 10, yawan kudin kamfanin a ketare ya kai dallar Amurka biliyan 40. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China